10 Afirilu 2021 - 01:04
Mutanen Da Suka Mutu A Sabon Rikicin Yankin Darfur Na Sudan Sun Kai Mutane 132

Adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon sabon rikicin da ya ɓarke a Geneina, babban birnin Lardin Yammacin Darfur na ƙasar Sudan sun kai mutane 132 kana wasu sama da 200 kuma sun sami raunuka.

ABNA24 : Gwamnan jihar Mohamed Abdallah al-Douma ne ya shaida wa manema labarai hakan inda ya ce a halin yanzu mutanen da suka mutu ɗin sun kai 132 sannan wasu 208 kuma sun sami raunuka.

Rikicin dai wanda ya faro tun daga ranar Asabar ɗin da ta gabata, shi ne rikici na baya-bayan a yankin na Darfur.

Yarjejeniyar sulhun da aka cimma a ƙarshen shekarar da ta gabata da kuma janyewar dakarun tabbatar da zaman lafiya na MDD, duk hakan dai bai kawo ƙarshe rikici da kuma zubar da jini a wannan yankin ba.

Yankin na Darfur dai ya sha fuskantar rikice-rikice tsakanin larabawa da sauran ƙabilund a suke wajen mafi yawa saboda rikici na ƙasa da kuma albarkatun ƙasar da ke yankin.

342/